Masarautar Katsina ta warware rawanin hakimin bakori, makaman Katsina

0
72

Masarautar Katsina ƙarƙashin jagorancin mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ta warware rawanin makaman Katsina, Hakimin Bakori daga sarauta.

Hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwar da Kauran Katsina, Hakimin Rimi Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir ya sanyawa hannu a madadin masarautar Katsina sannan aka raba wa manema labarai a Katsina.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ta warware rawanin makaman Katsina, Alhaji Idris Sule Idris ne bisa wasu korafe-korafe da masarautar ta samu inda ta gudanar da bincike kafin yanke wannan hukunci.

A cewar fadar mai martaba sarkin Katsina, kafin ɗaukar wannan mataki sai da majalisar sarkin Katsina ta samu wata takarda daga ofishin sakataren gwamnatin jihar mai lamba SEC/54/VOL.VI/1416 da ta amince da cewa bincike ya tabbatar da samu tsohon makaman Katsinan da laifin da ake zargin sa da aikatawa.

“Haka kuma binciken da masarauta ta gudanar ya nuna cewa duk wasu zarge-zarge da ake yi a kan tsohon makaman yana da masaniya akan su” wanda a cewar fadar sarki hakan na iya haifar da rashin zaman lafiya a yankin Bakori” in ji sanarwar.

Daga ƙarshe dai masarautar ta Katsina ta yanke shawarar sallamar makaman Katsina hakimin Bakori daga sarauta a jiya alhamis 19/1/2023, sannan ta yi fatan Allah ya ba da zaman lafiya.

Idan za a iya tuna masarautar ta Katsina ta dakatar da makaman Katsina hakimin Bakori Alhaji Idris Sule Idris a ranar laraba 23/11/2022 bisa wasu zarge-zarge da masautar ta ce an gabatar a gaban ta sai dai ba ta yi ƙarin haske a kan korafe-korafe ba har zuwa yanzu da aka kareshi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here