Sheikh Aminu Daurawa ya jagoranci fitar da ɗaurarru 14 daga gidan yari a Kano

0
56

Gidauniyar Darus Sunna Foundation, ƙarƙashin jagorancin shahararren malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta fitar da wasu ɗaurarru da ga gidajen yarin Kurmawa da Goron Dutse a jihar.

Sakataren kwamitin fitar da ɗaurarrun, Aisar Salihu, a wata sanarwar da ya fitar a Kano a yau Asabar, ya ce an fitar ɗaurarrun 14, da su ka haɗa da maza 13, mace 1.

A cewar sanarwar, an duba masu ƙananan laifuka ne da aka ci su tara amma su ka kasa biya, inda ya ce har ma waɗanda a ke bi bashi amma su ke zaman gidan kaso sakamakon sun kasa biya.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe Naira dubu 250 wajen biya wa wadanda su ka amfana ɗin tarar da a ke musu, inda kuma a ka rarraba musu kuɗaɗen mota zuwa unguwanni da garuruwan su, da kuma kuɗaɗen siyan magani ga marasa lafiyar cikin su da ya kai Naira dubu 28.

“Bayan nan kuma ƴan kwamitin sun yi musu nasiha a kan su guji sake aikata laifukan da su ka sanya a kan daure su a gidan yari.

“Sannan mun yi musu wa’azi da nasiha kan su zama mutanen kirki idan sun koma gidajen su,” in ji sanarwar.

Kwamitin ya kuma yi kira ga masu-hannu-da-shuni da sauran bayin Allah masu hali da su rika kai ziyara gidajen yari don ganin halin da ɗaurarru ke ciki da kuma taimaka musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here