An kama mutane 2 bisa laifin sace makiyayi a Ogun

0
103

Jami’an hukumar tsaro ta So-Safe Corps mallakin jihar Ogun sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da wani makiyayi.

Rundunar ta ce ta samu kira a ranar 20 ga watan Janairu cewa an yi garkuwa da wani makiyayi mai suna Oseni a Olorunda-Lukosi, Iro a karamar hukumar Owode-Egba yayin da yake kiwon shanunsa.

Kakakin So-Safe, Moruf Yusuf, a ranar Lahadi, ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin, Mohammed Lawal (20) – mazaunin unguwar Sharagi a Karaoke; da Sarafa Asimiu (25) – mazaunin Amusa Yusuf House, Oke-Aje, Ibadan, suma sun kwace ma su kudi N130,000 da takardun babur dinsa.

Yusuf ya bayyana cewa daga baya wadanda ake zargin sun nemi N4m a matsayin kudin fansa ga Oseni.

Ya ce, “Kwamitin ‘yan sintiri na So-Safe Corps sun mayar da martani a kan lokaci ya sa aka kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da su, yayin da sauran kuma suke a hannunsu duk da cewa an yi ta tseguntawa wurin,” yana mai cewa an mika su ga ‘yan sanda.

Ya kara da cewa an mika makiyayin da aka sace, wanda aka kubutar da shi ba tare da jin rauni ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here