An kama mutumin da ake zargi bisa kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna hari

0
54

‘Yan banga a garin Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja, sun kama wani da ake zargi mai suna Bello Yellow, da alaka da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

An kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar Lahadi lokacin da ya taso daga motar da ke kusa da tashar Motar Dan-Kogi.

Wani dan banga ya ce ‘yan banga na Miyetti Allah ne suka ga wanda ake zargin.

Ya ce, “Sun jawo hankalin mambobinmu da ke wurin dajin don neman taimako. An kama shi aka kai shi ofishinmu inda aka bincike shi aka tsare shi kafin a mika shi ga ‘yan sanda da misalin karfe 4 na safe.’’

Majiyar ta bayyana cewa a yayin binciken an gano tsabar kudi N103,000 a hannun sa, da kuma sandunan sigari guda uku da wata wuta.

Majiyar ‘yan bangan ta bayyana cewa jami’in ‘yan sandan shiyya na Zuba da kan sa ya zo ofishinsu tare da mutanensa domin dauko wanda ake zargin.

Ya ci gaba da cewa, “Duk da cewa ’yan banga Fulani sun bayyana sunan wanda ake zargin da Bello Yellow, amma ya kira kansa da Bature Shabe, kuma ya fito daga Ilorin a Jihar Kwara yana kan hanyarsa ta zuwa dajin Shenagu kusa da Zuba inda babban yayansa, Alhaji Shabe. ke zaune.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here