Karancin sabbin kudi: ’Yan kasuwa za su rufe kasuwanni a Kebbi

0
56

’Yan kasuwa a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi sun yanke shawarar rufe kasuwanni saboda karancin sabbin kudi, wanda hakan ya fara haifar da tsaiko ga harkar kasuwancin a jihar.

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa na Jihar Kebbi, Alhaji Umar Dangura Gwadangwaji, wanda ya bayyana haka, ya ce ’yan kasuwar sun yi kokarin ganin sun samu sabbin takardun Naira daga bankuna daban-daban amma lamarin ya ci tura.

A cewarsa, “Idan muka ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudade daga hannun abokan kasuwanci, wane banki ne zai karba daga wajenmu idan wa’adin ya cika,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Talata masu ababen hawa da masu sayar da abinci a cikin birnin Birnin Kebbi sun ki karbar tsofaffin takardun kudi daga hannun kwastomominsu saboda bankuna da masu sana’ar POS sun ki karbar tsofaffin kudaden.

Mutane da dama ne suka yi jerin-gwano a bakin injinan ATM daban-daban don cirar sabbin kudaden a Jihar.

“Tun ranar Litinin nake zuwa banki domin na ciro kudi na siya wa iyalina kayan abinci saboda babu wanda zai karbi tsohon kudin. Sai dai lamarin ba a cewa komai saboda na kasa samun kudin a ATM na banki,” in ji wani magidanci.

Yusuf Ali, wani mutum mai ajiya a bankin GTB ya koka kan cewa, “Dubi yadda nake yawo da tsabar kudi amma babu wanda zai karba saboda tsofaffin takardun kudi ne har yanzu na gaza samun sabbin daga banki.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here