An sauya kudin Naira ne domin yin zagon-kasa ga zaben 2023 – Tinubu

0
94

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar APC mai mulik, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matsalar karancin man fetur da kuma sauya fasalin takardar kudin Naira a matsayin wani shiri na yi wa zaben 2023 zagon-kasa.

Tinubu na magana ne a yayin yakin neman zabensa a birnin Abeokuta na jihar Ogun a wannan Larabar.

A cewarsa, ba sa san a gudanar da wannan zaben, suna son yi wa zaben zagon-kasa. Shin za ku bari hakan ya faru? Tinubu ya tambayi dandazon magoya bayansa da suka hallara a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta.

Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya lashi takobin cewa, ‘yan Najeriya za su yi tattaki har zuwa rumfunan kada kuri’u duk kuwa da karancin man fetur din.

Tinubun ya bayyana kwarin guiwar samun nasara a zaben mai zuwa duk kuwa da kirkirar karancin man fetur din da sauya fasalin takardar kudin Naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here