Nan da kwanaki kadan man fetur zai wadata ko ina – Kyari

0
53
Mele kyari
Mele kyari

Shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPC ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan matsin da suka sake tsintar kansu sakamakon karancin man fetur.

Shugaban kamfanin man, Mele Kolo Kyari ya tabbatar wa BBC cewa ana sa ran matsalar ta yanke cikin Æ´an kwanaki kaÉ—an masu zuwa.

Kalaman Mele Kyari a tattaunawar sa da BBC, na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma a Najeriya ke ci gaba da fuskantar dogayen layukan mai, musamman a manyan biranen Æ™asar.

Matsalar ta man fetur, wadda ta Æ™i ci ta Æ™i cinyewa tun a shekarar da ta gabata, na ci gaba da jefa al’ummar Najeriya cikin garari, yayin da babban zaÉ“en Æ™asar ke Æ™aratowa.

Sai dai Mele Kyari ya ce cikin kwanaki biyu masu zuwa za a samu sauki ko da wahalar bata kare ba baki É—aya domin hukumomi sun É—auki matakan da suka dace domin ganin an shawo kan matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here