2023: Na rasa laifin me na yi wa mutanen da suke cin amana ta — Tinubu

0
243

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce baya fushi idan an ci amanarshi.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a jihar Edo, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar a ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan na Legas ya kuma soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kuma bukaci al’ummar jihar Edo da su kwato jiharsu daga PDP

Tinubu yace: “Dole ne mu ceto jihar Edo. Na shirya tsaf don yin aiki tare da ku. Ku dauki fitila ku bi gida bayan gida don kwato jiharku.

 

“Kada ku yi fushi; fushi baya magance matsaloli. Cin amanata karfin guiwa ya ke karamin in kara dage damtse. In ka yaudare ni baya bata min rai, zan yi watsi da kai ne kawai.

 

“Dalilina na yin hakan shine, kai ba Allahna ba ne kuma kai ba mahaliccina bane.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here