Yadda sojoji suka yi wa mayakan Boko Haram luguden wuta

0
107

Rundunar hadin-guiwar da ke yaki da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ta sanar da kaddamar da wasu munanan hare-haren sama a makon jiya akan sansanonin mayakan ISWAP domin murkushe su a maboyarsu.

Wata sanarwar da rundunar mai dauke da sojoji daga Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi ta gabatar, ta ce an kaddamar da hare-haren ne na musamman akan matsugunin ‘yan ta’addar da ke dajin Matari a Najeriya, inda suke amfani da shi domin kai hare-hare a garuruwan Maine Soroa da Chetinari da Chetimari Wangou a cikin kasar Nijar.

Sanarwar ta ce, an kaddamar da hare-haren na musamman ne bayan da aka tsinkayo wasu ‘yan ta’adda akalla 50 tsakanin ranakun 27 da 28 ga watan nan, kuma sojojin Nijar ne suka kai harin tare da taimakon kuramen jirage masu sarrafa kansu.

Sanarwar ta ce, sakamakon wadannan hare-hare, bayan lalata sansanonin ‘yan ta’addar, an kuma kama 38 daga cikinsu, yayin da wasu da dama suka gudu.

Ya zuwa yanzu dai, babu wata majiya ta daban da ta tabbatar da wannan labarin.

Bayan kwashe sama da shekaru 10, har yanzu kasashen Najeriya da Nijar da kuma Chadi na ci gaba da fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram lokaci zuwa lokaci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here