Wani mutum mai da har yanzu ba’a iya tantance sunansa ba ya mutu a wani banki da ke Agbor a jihar Delta bayan ya tsaya a kan layi na tsawon sa’o’i.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a wani banki dake karamar hukumar Ika ta kudu a jihar Delta.
An ce abokin hulda da bankin ya mutu bayan ya jira tsawon sa’o’i don karbar katinsa na ATM a bankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce: “Ba wajen ƙoƙarin cire kuɗi ba ne abin ya faru; ya zo karbar katin ATM dinsa ne.”
Wani Omole Mike, ya wallafa hoton marigayin a Facebook ya rubuta: “Yanzu haka, da misalin karfe 1:30 na rana. Wani ya fadi ya mutu a bankin First Bank of Nigeria, Agbor Branch. Rana: 02-02-2023. Allah Ya Jikansa da Rahma“