Zulum ya caccaki CBN kan karancin Naira

0
81

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana babban bankin Najeriya a matsayin miyagu saboda wahalar da talakawa da marasa galihu suke samu wajen samun sabbin takardun kudi na naira a ATM.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zagayawa wasu bankunan kasuwanci na ATM a Maiduguri a ranar Juma’a sakamakon rahotannin da ke cewa na’urorin ba sa fitar da kudi.

“CBN ya yi muguwar aika aika ta yadda ya azabtar da talakawa da marasa galihu ta hanyar sanya su na tsawon sa’o’i suna yin layi a na’urorin ATM wadanda iya talakawa kai kake gani ba masu kudi ba” inji shi.

Zulum, wanda ya kuma yi wata ganawar sirri da manyan jami’an bankin na CBN reshen Maiduguri, ya yi matukar takaicin yadda talakawa da marasa galihu ne kawai aka samu a layukan na’urar ATM da ke kokarin fitar da ‘yan kudade don bukatun su na yau da kullum.

Gwamnan wanda ke da katikan ATM sama da 10 na wasu bankunan, ya yi watsi da batun  wa’adin canjin Naira idan CBN bai tabbatar da samun sabbin takardun kudi na banki ba.

“Rashin samun sabbin takardun shi ne matsalar,” in ji Zulum, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawarsa ta sirri da jami’an babban bankin, inda ya koka da cewa, “Mun saki Naira biliyan 5 na albashin watan Janairu, amma ATM ba sa rabawa saboda babu kudi.”

Gwamnan wanda ya ce ya za ka ga na’urorin ATM kusan 10 ne ba tare da ya ga wani attajiri a cikin jerin gwano ba, ya koka da yadda harkokin kasuwanci a fadin jihar ya gurgunta sakamakon rashin samun kudaden da ke zagawa a fadin jihar, sakamakon yadda ake fuskantar matsalar samun sabbin takardun kudi a banki.

Ya kuma yi kira ga CBN da ya tabbatar da samar da takardun kudin domin jama’a musamman talakawa da marasa galihu su sa mu.

“Ina jajantawa al’ummar yankin saboda karancin sabbin takardun kudi,” in ji shi, inda ya yi alkawarin mika matsalolin su ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), domin ya umurci CBN ya tabbatar da samun sabbin takardun.

Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba a reshen Maiduguri na CBN ta shaida wa jaridar PUNCH cewa babban bankin ya raba wa bankunan kasuwanci da ke jihar Naira biliyan 9 a cikin wata daya da ya gabata.

“Don haka ya kamata gwamna ya zargi bankunan kasuwanci da rashin samun sabbin takardun kudi a na’urar ATM, ba CBN ba,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here