Farashin abinci ya rikito a Najeriya saboda rashin takardar Naira

0
71

Farashin kayayyakin abinci a wasu kasuwannin Najeriya ya fara rikitowa sakamakon karancin takardun kudaden Naira a sassan kasar, lamarin da ya tilasta wa da dama daga cikin ‘yan kasuwa jingine harkokinsu na wucIn-gadi.

A hirarsa da RFI Hausa, shugaban Kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, Alhaji Muttaqa Isa, ya tabbatar da faduwar farashin kayayyakin abincin , yana mai cewa, rashin madarar kudi a hannun mutane, shi ne ya janyo saukar farashin.

Bayanin Alhaji Isa.

Alhaji Isa ya kara da cewa, wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun daina sayar da hajarsu har sai an biya su da tsabar kudi, abin da ke nuna cewa, ba su gamsu da tsarin nan na hada-hadar kudade ta yanar gizo ba.

Ba kowanne dan kasuwa ne ke amincewa a tura masa kudi ta intanet ba saboda rashin sabo gami da fargabar damfara.

Ita dai gwamnatin Najeriya na son ‘yan kasar su mayar da hada-hadar kudadensu na kasuwanci kacokan kan yanar gizo, lamarin da ta ce zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin kasar.

Sai dai babban kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu, shi ne, ba kowa ba ne ya iya sarrafa wayarsa ta fuskar tura kudade daga  asusun bankinsa zuwa wani asusu na daban, yayin da wasu ma ba su da asusun bankin ma baki daya, inda suka saba saye da sayarwa da tsabar kudi zalla a hannu.

Wannan  na zuwa ne bayan Babban Bankin Kasar na CBN ya sauya fasalin tsoffin takardun Naira da suka hada da Naira 1000 da 500 da 200.

Da dama daga cikin ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wadatattun takardun kudin Naira hatta a bankuna da na’urar cire kudi ta ATM, abin da ya jefa kasar cikin wani yanayi na wahala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here