Hukumar aikin Hajji kasa ta warewa kowacce jiha gurbin mahajjatanta

0
143

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce ta raba kason kudin aikin hajjin shekarar 2023 ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi 36, da babban birnin tarayya Abuja da kuma rundunar soji.
Mataimakin daraktan yada labarai da yada na hukumar, Mousa Ubandawaki, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ranar Asabar a Abuja.

Ya ce an cimma matsayar ne a karshen taron kwamitin zartarwa wanda ya amince da kason.

Ubandawaki ya lissafo kujerun ga jihohin kamar haka: Abia 53, Adamawa 2,669, Anambra 39, Bauchi, 3,132, Bayelsa 35, Benue 236, Borno.2,735, Cross River 66, Delta 74 and Nassarawa 1,567.

Ya ce sauran jihohin sun hada da: Niger 5,165, Ogun 1,139, Ondo 436, Osun, 1,054, Oyo 1,441, Yobe 1,968, Ebonyi 117, Edo 274, Ekiti 197, Enugu 40, FCT 3,520 and Gombe, 2,30

sauran sune Imo 30, Jigawa 1,525, Kaduna 5,982, Kano 5,902, Katsina 4,913, Kebbi 4871, Kwara 3,219, Lagos 3,576, Plateau 1,984, Rivers 50, Sokoto 5,504, Taraba 1,590, Zamfara 3,083 rundunar sojin Najeriya 543.

Ya bayyana cewa za a fitar da kason na Kogi bayan kammala nazarin ayyukan ta.

Ubandawaki ya ce an dakatar da rabon na Akwa Ibom ne saboda rashin sabunta lasisin aiki.

Ya kuma ce ana sa ran dukkan jihohin za su biya kashi 50 cikin 100 na kujerun 2023 da hukumar NAHCON ta basu kafin wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

“Rashin cika sharuda ga kowace jiha na cika wa’adin zai haifar da raguwar rabon kujeru ga irin wannan jihar,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here