Kai karuwa ne a siyasa, Keyamo ya caccaki Yakubu Dogara

0
48

Kakakin majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Festus Keyamo, ya bayyana tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a matsayin ‘karuwar siyasa’.

Keyamo ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, keyamo, na mayar da martani ne kan wani sako da Dogara ya yi tun farko a shafinsa na Twitter.

Dogara ya yi nuni da goyon bayan shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yin  yakin neman zabe a jihar Nasarawa.

“Na san cewa Buhari na son barkwanci amma ban san barkwancin zai kai ga haka ba. Asiwaju zai ba da mafi kyawun shugabanci ga yan Najeriya? Da Takaddun shaidar karatu na karya? da sauran halaye na rashin da’a?. haba Buhari, Nijeriya ba ta cancanci irin wannan daga wajenka ba,” Dogara ya fada ta cikin sakon twitter.

Sai dai Keyamo ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya kira Dogara a matsayin mai yawon ta zubar irin na shiyasa.

Ya rubuta, “Yayana kuma abokin karatuna kuma lauya, @YakubDogara, Haƙiƙa na san ba ku ji daɗin goyon bayan shugaban kasa Buhari ga Bola Tinubu ba, shugabannin biyu sun tsaya tsayin daka ga imaninsu da manufofinsu domin yiwa Najeriya hidima, ba kamar kai karuwan siyasa ba, mai yawo da ƴan daba a ko yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here