Za’a mayar da dajin Faskari wurin shakatawa na gwamnatin tarayya

0
121

Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da kwamitin gudanarwa na kafa wajen shakatawa a dajin kogo na karamar hukumar Faskari.

Mataimakin gwamnan jihar QS Mannir Yakubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa yin amfani da gandun daji yadda ya kamata zai kiyaye halittu da kuma inganta tasirin sauyin yanayi a jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce jihar tana albarkar dan adam da albarkatun kasa da ya kamata a yi amfani da su domin tabbatar da ci gaban jihar.

Tun da farko babban jami’in kula da gandun dajin na kasa Dr Ibrahim M Goni ya ce kwamitin gudanarwar zai taimaka wajen mikawa da kuma daukar nauyin aikin dajin Kogo da aka ware a karamar hukumar faskari.

Ya bayyana cewa shugaban kasa

Muhmmadu Buhari a watan Nuwamba 2020 ya amince da kafa karin wuraren shakatawa na kasa guda goma ga bakwai da ake da su wanda ya kawo adadin zuwa goma sha bakwai a kasar.

Ya kara da cewa tun a shekarar 1992 aka fara tattaki na kafa sabbin wuraren shakatawa na kasa bayan da aka kafa doka 36 da ta kafa wuraren shakatawa na kasa biyar na farko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here