Gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara sun maka gwamnatin Tarayya a Kotu

0
154

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a yau litinin ne Gwamnonin 3 da suka kunshi Malam Nasir El Rufa’i da Bello Matawalle da kuma Yahaya Bello suka maka gwamnatin Najeriyar a gaban kotun kolin kasar don dakatar da sauya fasalin kudin kasar biyo bayan wahalhalun da ‘yan Najeriya suka shiga sakamakon sauyin takardun kudin na Naira 200 da 500 da kuma 1000.

Wadannan gwamnoni uku sun dauke matakin da suke gani ya dace da samar da mafita kan wahalhalun da al’ummar jahohin su ke fuskanta a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here