Karancin mai: Masu sufuri sun yi barazanar zanga-zanga a hedkwatar NNPC

0
142

Gamayyar kungiyoyin masu safara sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga a hedikwatar kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) saboda karancin man fetur.

Sanarwar da suka fitar a ranar Litinin ta samu sa hannun Jamilu Mai Alheri, Shugaban kungiyar Direbobin Tirela (TADAN), da wasu sauran kungiyoyi biyar.

Su ne Kungiyar Masu Keke Mai kafa uku ta Najeriya (TOWAN), Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Nijeriya (NASTAN), Ƙungiyar Motocin Kasuwanci ta Nijeriya (COMAN).

Sauran sun hada da Kungiyar Mata ‘yan Kasuwa ta Najeriya (MAWAN), da kungiyar matuka motocin tireloli ta kasa (TADAN), da masu tuka motocin safa safa (LUBOU).

Kungiyoyin dai sun sanya mambobinsu a fadin kasar nan cikin shirin ko ta kwana domin shiga zanga-zangar idan har ba a yi wani abu ba don kawo karshen karancin man.

Kungiyoyin sun ce za su ci gaba da mamaye manyan gine-ginen NNPCL da ke Abuja har sai an gyara matsalar.

Sun kuma yi barazanar cewa ba za su samar da motocinsu don jigilar kayayyakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) don gudanar da zaben ba.

Kungiyoyin sun koka da cewa karancin man fetur da ake fama da shi ya jefa su cikin wani hali da ba za su iya jurewa ba.

Sanarwar ta ce mambobin sun dogara ne kan samun kudin shiga na yau da kullun daga ayyukansu wanda abin ya shafa.

“Har ila yau, za a yi la’akari da cewa ana sayar da man fetur a gidajen man da ba gwamnati ce ta amince da su ba a kan Naira 350 zuwa N400 kan kowace lita.

“Wannan ya tilasta wa yawancin mambobinmu barin motocin bas, babura da sauransu,” in ji ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here