Babu wanda zai samu kuri’u miliyan 1.9 da Buhari ya samu a Kano a 2015 – Datti Ahmed

0
89

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce sama da kuri’u miliyan 1.9 da shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya samu a jihar Kano a zaben 2015, ba dan takara zai samu wannan kuri’u a zabe mai zuwa.

A shekarar 2015, Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress, ya doke jam’iyyar PDP ta Goodluck Jonathan da kuri’u 1,903,999, yayin da shi kuma ya samu kuri’u 215,779 a Kano.

“Kuri’un arewacin Najeriya da suke jiran a samu rarrabuwar kawuna wanda ko wanne daga cikin biyun da suka zo na biyu ke fatan samu, ya zama ba su samu ba,” in ji Baba-Ahmed a yayin wani shiri kai tsaye a gidan talabijin na Channels. Shirin zabe na musamman na Talabijin Hukuncin 2023 a ranar Talata.

“Masu kaikayi – misali Kano – yanzu ba kamar 2015 ba ce na yadda kuri’arta a  shekarar 2015, kuri’u miliyan 1.9 na Kano, babu wanda zai yi kwadayin samunta ko shakka babu sai Buhari in da ya yiwa Jonathan wanwar. Babu wanda zai samu haka a Kano a 2023.”

Baba-Ahmed ya ce sauran shiyyoyin da ake fafatawa a Arewa sune Kaduna da Katsina.

Kamar yadda gidan Talabijin din Channels ya ruwaito, wasu abubuwan da ya yi imanin suna taimaka wa jam’iyyarsa sun hada da bunkasar matasa a jiharsa ta Kaduna, da kara wayar da kan jama’a kan hada kan Najeriya, da kuma wadanda’yan asalin yankin  Kaduna ta kudu ne .

“Muna da jama’a mai yawa fiye da sanin abokan takarar mu,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here