Hukumar gudanarwar Firimiya na tuhumar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da karya dokokin hada-hadar kudi wajen cinikin ‘yan wasa da biyan albashi, laifukan da ake ganowa bayan gudanar da binciken shekaru 4.
Firimiyar ta ce Man City ta aikata laifukan ne a shekarun 2009 da 2018, inda ta yi zargin cewa tun bayan faro binciken kungiyar ta gaza bayar da hadin kai ga mahukunta duk da zarge-zargen karya ka’idoji 100 da ake mata
Wannan tuhuma dai za ta iya janyowa Manchester City cin tara ko kuma rage maki koma korarta daga take leda a gasar ta Firimiya gabaki daya dai dai lokacin da ta ke kokarin kare kambunta na firimiya da Arsenal ke shirin kwacewa.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta yi maraba da binciken na Firimiya wanda ta ce ta yi matukar mamaki da yadda firimiyar ke ci gaba da tuhumarta da wannan laifi tana mai cewa akwai bukatar kawo karshen wannan matsala a tsakaninsu.
A kakar da ta gabata ne, Manchester City ta dage kofin Firimiya na 6 tun bayan karbar ragamar da tawagar ‘yan kasuwar Abu Dhabi suka yiwa Club din a 2008.
Manchester City wadda ta zuba makuden kudade wajen gina Club din da manyan ‘yan wasa da kuma tawagar Manajoji daga 2008 zuwa yanzu taki amincewa da bayar da takardu ko kuma bayanan da ke kunshe da wannan ciniki wanda Firimiya ke ganin kungiyar ta kashe kudin da ya wuce kima musamman a kakar wasa ta 2009-2010 da kuma 2012-2013 lokacin da Roberto Mancini ke jagorancinta sai kuma 2015-2016.
Ko a shekarar 2020 sai da hukumar UEFA ta samu Manchester City din da makamantan wadannan tuhume-tuhume.