Yadda gobara ta kone gidan mai

0
126

Wani gidan mai ya kone bayan tashin gobara da ta kama injinan bayar da mai da wani gini da ke harabarsa a garin Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Kakakin Hukumar a jihar, Ayodele Ajulo, ya ce wutar ta tashi ne sakamakon zafi da tankin ajiye mai a karkashin kasa ya dauka.

Ajulo wanda ya yi magana bayan kashe gobatar, ya ja hankalin masu gidajen mai da su rika yin hattara a duk lokacin da ake sauke mai zuwa tankunansu da ke karkashin kasa.

“Mun sha jan hankalin mutane musamman a wannan yanayi na zafi, saboda wuta ta kan tashi cikin sauki.

“Yana da matukar muhimmanci musamman ga masu gidajen mai da  su rika daukar dukkan matakan kariya don kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi,” in ji shi.

Ya jinjina wa mazauna yankin da suka taimaka wajen ganin an kashe gobarar ba tare da an yi asarar rai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here