Yadda ’yan Boko Haram da ISWAP suka kashe juna a Borno

0
116

Mayakan Boko Haram da na ISWAP sun hallaka juna a wata arangama tsakanin kungiyoyin ’yan ta’addan domin kwace iko a yankin Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi.

’Yan ta’adda da dama kuma sun samu raununka a artabun da suka yi a kauyukan Nguro da Ngoldiri da ke yankin Timbuktu Triangle a Damboa, Jihar Borno.

Arangama ta wakana ne da misalin karfe 12 na dare a daidai lokacin da kungiyar ISWAP ta kai hari kan wasu mayakan Boko Haram da ke tafiya.

Rikicin baya-bayan nan na ranar 7 ga watan Fabrairun 2023 a Timbuktu wanda ya dauki tsawon awanni 3 ana yi, ya yi sanadin mutuwar mayaka da dama daga kungiyoyin ta’addan.

Yayin da ake kara samun hare-hare tsakanin ISWAP da Boko Haram, an gano cewar ISWAP na shirin kaddamar da wasu hare-hare a yankin Dajin Sambisa, Marte da Abadam don kwato wasu yankuna daga Boko Haram.

A gefe guda kuma Boko Haram na yin tattaki a Dajin Sambisa da tsaunin Mandara domin fuskantar ’yan ta’addar ISWAP.

Don sake farfado da karfinta na yaki, Boko Haram ta nada wani Alhaji Ali Hajja Fusam, dan asalin Bama a matsayin sabon shugabanta a Gaizuwa, sansanin da sojojin Operation Hadin Kai suka sha lalatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here