Kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta soke taron yakin neman zaben shugaban kasa da ta shirya yi a jihar Kano karo na biyu.
Jaridar Daily News 24 ta rawaito cewa Sakataren kungiyar yakin neman zaben, James Faleke a wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Alhamis, ya ce an soke taron da aka shirya yi a ranar 16 ga watan Fabrairu.
Mista Faleke bai bayar da wani dalili na soke taron ba. Gangamin dai ya gudana ne a ranar 4 ga watan Janairu a Kano a filin wasa na Sani Abacha amma bisa jadawalin jam’iyyar ya kamata Kano ta karbi bakuncin jam’iyyar har sau biyu.
Babu tabbas ko soke taron bai da alaka da kukan da ake yi kan karancin Naira.