Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce kusan kashi 90 cikin 100 a shirye ta ke don gudanar da babban zaben 2023.
Mista Auwal Mashi, sakataren hukumar INEC na Jihar Kaduna ne, ya bayyana haka a ranar Alhamis a taron masu ruwa da tsaki a Mellinium Hope, a Kaduna.
Mashi ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kammala shirye-shiryenta don tabbatar da aiki da ingancin injin BIVAS.
“A cike da gamsarwa, injinan na da kyau.
“Ina mai tabbatar muku da cewa in Allah ya yarda ba za mu samu matsala da injinan mu ba,” in ji shi.
Mashi ya ce kimanin sabbin katunan zabe 408,000 da wasu 228,000 da aka kwashe daga wasu wurare ne masu su suka karba.
Ya ce an riga an tanadi muhimman kayyakin zaben daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Mashi ya ce INEC ta hada kai da CBN domin ganin an samu kudaden gudanar da zaben ba tare da tangarda ba.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya rawaito cewa taron ya kunshi tambayoyi da amsoshi kuma mahalarta taron sun hada da ‘yan siyasa, shugabannin gargajiya da na Addinin da dai sauransu.