A kama duk mutumin da ya ki karbar tsofaffin kudi — Gwamnan Zamfara

0
136

Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya bayar da umarnin kama duk mutumin da ya ki karbar tsofaffin takardun kudi a jihar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar, gwamnan ya ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta bayar da hukuncin karshe game da karar gwamnonin Arewacin kasar uku suka kai gabanta suna kalubalantar matakin.

A makon da ya gabata ne dai Gwamnonin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka kai Babban Bankin Najeriya CBN da Gwamnatin Tarayya kara gaban Kotun Kolin kan batun wa’adin amfani da tsoffin takardun kudin kasar.

Gwamna Matawalle ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake rantsar da Alkalan Babbar Kotun Jihar da sabbin masu ba shi shawara na musamman a Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnan ya ce sun je Kotun Kolin ne shi da takwarorinsa na jihohin Kaduna da Kogi, inda suka bukaci kotun da ta bayar da umarnin kara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin.

Ya kara da cewa “Wannan mataki da Kotun Koli ta dauka ya taimaka wajen kare kasar nan daga fadawa cikin rikice-rikice, wadanda ka iya shafar zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar, lamarin da zai iya shafar babban zaben kasa da aka shirya gudanarwa cikin wannan wata.”

Gwamnan ya kuma bayyana farin cikinsa game da ci gaba da amfanin da tsofaffin takardun kudin kasar a harkokin kasuwanci da hada-hadar yau da kullum.

“Muna gode Wa Allah kasancewar mutane za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin a harkokin kasuwanci domin samun abun biyan bukatunsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba” in ji Matawalle.

A Juma’ar da ta gabate ce Majalisar Koli ta Kasa wato Council of State, ta kammala wani taron gaggawa a Fadar Shugaban Kasar da ke Abuja, inda ta bukaci Babban Bankin Najeriya, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin amfanin al’ummar kasar.

A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama’a tsofaffin takardun kudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here