Jerin ‘yan wasan da kwantirangin su zai kare a karshen kakar bana

0
92

A karshen watan janairun wannan shekarar ta 2023 aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a wasu kasashen Turai, sai kuma karshen kakar nan za a ci gaba da hada-hadar kaka ta gaba.

To sai dai kuma kamar yadda doka ta tanada kungiyoyi za su iya sayen wadanda kwantiraginsu zai kare zuwa karshen kakar nan wanda hakan yake nufin kungiya za ta dauki wanda yarjeniyarsa ta kusan karewa zuwa karshen kakar nan da wanda ba shi da wata kungiyar da yake da yarjejeniya da ita.

Cikin ‘yan wasa da ke kasa a yanzu akwai Isco, shi ne wanda ke da kwarewa da yawa, bayan lashe kofuna da yawa a kungiyar Real Madrid dan kwallon tawagar Sifaniya ya lashe kofin zakarun turai na Champions League guda biyar da Club World Cup guda hudu da La Liga uku da Uefa Super Cup uku da Copa del Rey.

A cikin watan Disamba dan wasan da Sevilla suka amince kowa ya kama gabansa, an kuma sa ran a karshen Janairu zai koma kungiyar kwallon kafa ta Union Berlin daga baya batun ya bi ruwa yayin da wakilinsa ya yi wa Manchester United tayin dan wasan bayan jin ciwon Cristian Eriksen.

Jerin wasu ‘yan wasan da za a iya dauka a wannan lokacin;

Sime Brsaljko dan kasar Croatia, mai tsaron baya, mai shekara 31 da Jese Rodriguez dan kasar Spain, mai tsaron baya, mai shekara 29 da Federico Fernandez dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 33.

Akwai kuma Jordan Lukaku dan kasar Belgium, mai tsaron baya, mai shekara 28 da Bojan Krkic dan kasar Spain, mai cin kwallaye, mai shekara 32 sannan akwai Jurgen Locadia dan kasar Netherlands, mai cin kwallaye, mai shekara 29 sai Renzo Sarabia dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 29 da Pape Cheikh Diop dan kasar Senegal, mai wasa daga tsakiya, mai shekara 25.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here