Mutumin da ya harbi saurayin kanwarsa a matsayin gargadi

0
171

Wani mutum mai suna Michael Ogundele, mai kimanin shekara 30 da ke zaune a Idiroko,ta karamar hukumar Ipokia jihar Ogun, ya harbi saurayin kanwarsa mai suna Tobi Olabisi.

‘Yansanda sun samu nasarar kama Ogundele, bayan an kararsa ofishin ‘yansanda da ke Idiroko.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda na jihar, Abimbola Oyeyemi,ya ce, wasu mutane sun zo da wani mutum ofishin ‘yansanda domin kawo kararsa kana bin da ya yi.

Kamar yadda Oyeyemi, Akeem ya ce, ya harbi mutumin ne, saboda ya ki jin gargadin da ya yi masa na ya daina soyayya da kanwarsa.
An ce, yin kunnen kashi da wannanan umarni, ya kai masa hari da niyyar ya kashe shi, amma dai sai ya tsallake rijiya da baya.

Kamar yadda DPO Alfa Akeem, ofishin Idiroko, CSP Ayo Akinsowon,ya ce, bayan samun wannan labarin sai ya gaggauta shirya jama’arsa, suka tafi inda wannan abin ya faru, wadanda kuma suka yi nasarar kama wanda ake zargin.

Lokacin da ake bincikar wanda ake zargin, ya ce, kafin hakan ya faru, sai da ya ta gargadin wanda abin ya rutsa da shi, kan ya daina zuwa wajen kanwarsa,amma sai ya burus da wannan umarni, kamar yadda Oyeyemi ya ce.
Wanda ake zargin, a wata rana,ya salabarin cewa Olabisi yana zuwa dakin kanwarsa ya kwanta yana bacci, saboda haka, sai ya dauki makami, ya lallaba, don ya kai masa hari.

Ya kuma same shi a daki, amma da ya tabbatar da cewa, za a iya kashe shi, sai ya yi kukan kura, ya fita daga daki, ya kuma ce, kafa main a ci ban ba ki ba !.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here