Ronaldo ya kafa wani sabon tarihi bayan jefa kwallaye 4 a raga

0
169

Tauraron kwallon kafar duniya Cristiano Ronaldo ya sake kafa wani sabon tarihi na zirara kwallaye sama da 500 da wani ‘dan wasa guda ya taba yi, bayan ya jefa kwallaye 4 wa kungiyarsa ta Al Nassr dake Saudi Arabia a karawar da suka yi da Al Wehda a gasar lik-lik na kasar.

Wadannan kwallaye guda 4 sun kai adadin kwallayen da Ronaldo mai shekaru 38 ya jefa a rayuwarsa zuwa 503 a kungiyoyin kwallon kafa 5 da ya yiwa wasa.

Alkaluma sun nuna cewar Ronaldo ya jefa kwallaye 3 wa kungiyar Sporting Lisbong ta Portugal da 103 wa Manchester United a Ingila sai kuma 311 wa Real Madrid da 81 wa Juventus.

Bayan rattaba hannu wa kungiyar Al Nassr, Ronaldo ya jefa mata kwallaye 5, abinda ya kawo adadin kwallayensa zuwa 503.

Tauraron ‘dan wasan ya kuma kafa tarihin jefa kwallaye 3 har sau 61 a rayuwarsa, sakamakon kwallaye 4 da yaci a yammacin jiya.

Sau 5 ‘dan wasan na Portugal ke lashe kyautar ‘dan kwallon da yafi kowa bajinta a duniya da ake kira Ballon d’Or.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here