HomeLabaraiLabaran DuniyaWakilin Sin ya yi kira da a gina budadden tsarin raya tattalin...

Wakilin Sin ya yi kira da a gina budadden tsarin raya tattalin arzikin duniya

Date:

Related stories

Abba gida-gida ya lashe zaben gwamnan Kano

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta sanar da cewa...

INEC na neman ta ce zaben gwamnan Kano ‘Inconclusive’ ne — Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, sanata Rabiu...

Zaben gwamnan Kano: Ratar kuri’ar da ke tsakanin NNPP da APC

Bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 44 na zaben gwamnan...

Jami’in tattara sakamakon zabe ya yanke jiki ya fadi a hedikwatar INEC a Kano

Jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Muhammad Yushau na karamar...

Sakamakon zaben gwamnonin jihohin Najeriya

Wannan shafin zai rika kawo muku kammalallen sakamakon zaben...

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Dai Bing, ya gabatar da jawabi a wata muhawarar da aka yi a taro na 61 na kwamitin kyautata zaman rayuwar al’umma na majalisar, inda ya yi kira da a aiwatar da tsarin kasancewar bangarori daban-daban, da gina wani budadden tsarin raya tattalin arzikin duniya.

Dai ya ce, duniya na fuskantar manyan sauye-sauye da ba’a taba ganin irinsu ba tsawon shekaru da dama, inda ake bukatar hadin-kan kasa da kasa don shawo kan matsaloli. Dai ya yi kira da a gina wani budadden tsarin bunkasa tattalin arzikin duniya, da samar da kayayyaki ba tare da matsala ba, da adawa da nuna bambancin ra’ayi ga sauran kasashe, ko kuma katse huldar hadin-gwiwar kasa da kasa.

Ya ce ya kamata kasashe masu hannu da shuni su sauke nauyin dake wuyan su, kana, kasashe masu tasowa su zurfafa hadin-kai a tsakaninsu, kuma dukkan bangarorin biyu su hada gwiwa don zama tsintsiya madaurinki daya, da raya huldar abokantaka mai hadin-gwiwa da daidaito da adalci, wadda ke iya samar da alfanu ga kowa da kowa, wato kar a bar kowace kasa da kowane mutum a baya. (Murtala Zhang).

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here