AIG Lawan Tanko Jimeta ya rasu bayan ‘yar gajeruwar jinya

0
106

Mataimakin Sufeto Janar (AIG) na ‘Yansanda mai kula da shiyya ta 5 da suka hada da jihohin Edo, Delta da Bayelsa, Lawan Jimeta ya rasu.

Ya rasu ne da safiyar Lahadi a Asibitin Koyarwa na Benin, Jihar Edo bayan gajeruwar rashin lafiya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wani sako da ya aike ta Whatsapp ranar Lahadi.

Ya ce: “Inna Lillahi wa inna ilaihi raji’un. Cikin alhini da raunin zuciya nake sanar da rasuwar A.I.G Lawan Tanko Jimeta. gaba daya muna mika wuya ga Allah Ta’ala,

“Ya rasu ne a asibitin koyarwa na jihar Benin Edo da safiyar yau Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya.

“Ga Allah muke, kuma gare shi za mu koma.

“Allah Ta’ala Ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da aljannatul fiddausi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here