Canjin kudi: Gwamnatin Neja ta maka gwamnatin tarayya a kotu

0
126

Gwamnatin Neja ta maka gwamnatin tarayya kan tsarin canjin kudi da babban bankin tarayya a babban kotun tarayyar Nijeriya ya bullo da shi.

Bayanin karar na kunshe cikin wata takarda da aka ba manema labarai da kwamishinan shari’a, Br. Nasara Danmallam, ya gabatar a takardar karar mai lamba SC/CV/210/2023 wanda aka gabatar ranar 10 ga watan Fabrairun 2023, akan korafin gwamnatin jiha, inda ta bukaci da a kara wa’adin da babban bankin tarayya ya bayar na daina karbar tsoffin kudaden naira #200, #500 da naira #1000.

A cewarsa, shigar da karar da gwamnatin jihar ta yi ya biyo goyon bayan rashin wadatuwar sabbin kudaden da ake son maye gurbin tsoffin da ya janyo matsananciyar wahala da jama’a suka fada a jihar, musamman wadanda ke yankunan karkara.

Antoni janar kuma kwamishinan shari’ar ya baiwa al’umar jihar tabbacin gwamnatin jiha ta damu matuka akan a korafe-korafensu, kuma ya basu tabbacin gwamnatin jihar zata ci gaba da bin matakan doka dan ganin sun fita cikin wannan kuncin da canjin kudin ya janyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here