Mun yi wa dalibai Miliyan 1.1 rajistar jarabawar shiga manyan makarantu a bana – JAMB

0
98

Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta ce kawo yanzu, ta yi wa dalibai sama da miliyan 1.16 da ke son shiga manyan makarantu rajistar jarabawar UTME.

Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka lokacin da yake zagayen duba wasu cibiyoyin zana jarabawar ranar Asabar a Abuja.

Sai dai ya ce ko kadan ba za su kara wa’adin rajistar ba ga dalibai, sannan ya gargadi masu yin rajistar daga tatsar kudaden da ba gaira ba dalili.

An dai fara sayar da fom din ne ranar 14 ga watan Janairun 2023, kuma ana sa ran kammalawa ranar 14 ga watan Fabrairu.

A cewar Farfesa Ishaq, “Ana ci gaba da yi rajista kamar yadda ya kamata, I’m ban da wata makaranta da muka kama tama karbar Naira 30,000 a matsayin kudin rajista, sannan duk da haka su je suna yi musu kuskure a wajen rajistar.

“Wannan rashin imani ne kuma za mu dauki kwakkwaran mataki a kan irin su.”

Daga nan sai ya bukaci duk wanda ya fuskanci wannan matsalar da ya kai kara ga hukumar, inda ya ce har lada za su ba shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here