Na yanke kauna daga mutanen da ke zagaye da Buhari – El Rufa’i

0
103

A yayin da zaben shugaba kasa ya rage kasa da mako biyu, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya sare game da nagartar mutanen da ke zagaye da Shugaba Muhammadu Buhari.

El-Rufai ya fasa kwan ne kwanaki kadan bayan ya tayar da kura a lokacin da ya yi zargin cewa akwai wasu jami’ai a Fadar Shugaban Kasa da ke makarkashiya ga takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na Jami’iyyar APC.

A wata hira ta musamman da kafar yada Labarai ta PREMIUM TIMES, El-Rufai ya ce, “Na yi amanna da Buhari kuma har gobe ina tare da shi.

“Amma mutanen da ke zagaye da shi, na yanke kauna daga gare su lura da irin matakai da tsare-tsaren da suke fitarwa.”

Tuni dai kafar ta fitar da tsakuren hirar da ta yi da El-Rufai ta Twitter a ranar Lahadi.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya a wata hira da ya yi da tashar Talabijin ta Channels, El-Rufai ya zargi wasu wasu mutanen da suka goya wa wanin Tinubu baya a zaben dan takarar shugaban kasa sun koma shiga rgiar Buhari domin biyan bukatunsu.

A cewarsa, “Na yi amanna cewa a Fadar Shugaban Kasa akwai mutanen da ke so mu fadi zabe saboda hakarsu ba ta cim ma ruwa ba; Suna da dan takararsu, amma bai kai labari ba a zaben fid-da-gwani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here