Kwana 10 kafin zaben shugaban kasa, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen rumfunan zabe 124 da ta soke.
INEC ta ce ta soke rumfunan zaben ne a wasu jihohi 15, saboda babu ko mutum daya da ke da rajista a cikinsu, don haka, ba za a yi zabe a nan ba a wannan karon.
Jerin sunayen rusassun rumfunan zaben da INEC ta fitar ya nuna Jihar Imo ce a kan gaba da rumfunan zabe 38 da ka soke.
Ga jerin jihohin da abin ya shafa da kuma yawan rumfunan zabensu da INEC ta soke:
- Imo – 38
- Abia – 12
- Borno – 12
- Binuwai – 10
- Kano – 10
- Kaduna – 8
- Anambra – 6
- Bauchi – 6
- Adamawa – 4
- Delta – 4
- Ebonyi – 4
- Enugu – 4
- Jigawa – 3
- Bayelsa – 2
- Edo – 1.
A ranar 25 ga watan Fabrairu da muke ciki ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa na da Majalisun Tarayya, wanda bayansa da mako biyu za a gudanar da na gwamnoni da Majalisun jihohi a ranar 11 ga watan Maris, 2023.