Zaben 2023: DSS ta gargadi ‘yan siyasa kan kalaman tunzura jama’a

0
102

Gabanin zaben shekarar 2023, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadi ‘yan siyasa kan kalaman da ba su dace ba za su iya zafafa harkokin siyasa kafin da bayan zabe.

Hukumar ta DSS ta bayyana hakan ne biyo bayan zargin yunkurin juyin mulkin da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode ya yi. Kakakin hukumar ta DSS, Dakta Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata, ya ce: “An shawarci jam’iyyun siyasa da kakakin yada labaransu da su yi amfani da damar da za su bi wajen sawa ayi zabe cikin lumana.

A bisa gayyatar Fani-Kayode da kuma tattaunawa da hukumar DSS a ranar Litinin, Afunanya ya ce: “Hukumar DSS na son sanar da jama’a cewa ta gayyaci Femi Fani-Kayode hedkwatarta ta kasa, Abuja a ranar 13 ga Fabrairu, 2023.

Gayyatar ta kasance ne dangane da binciken wasu zarge-zargen da ya yi da kuma batanci da suka shafi harkokin tsaron kasa. “Fani-Kayode ya fuskanci tuhuma wanda ya yi hira da shi kan batun. Bayan haka, Hukumar ta ba da belinsa kuma ta umurce shi da ya koma ofis dinta daga ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023 har zuwa wani lokaci don a ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here