CBN ta bada lambobin da za’a kai karar masu POS dake chajin da ya wuce kima

0
198

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya saki lambobin wayar gaggawa ga jama’a don kai rahoton masu POS da ke siyar da sabbin naira da kuma wadanda ke chajin kudi da yawa yayin cire kud.

 Daraktan Sashen Gwamnan CBN, Mista Josph Omayuku, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a ranar Talata, 14 ga watan Fabrairu, makar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Yayin da yake gargadin masu aikata abubuwan da basa bisa ka’ida a kan su daina, Omayuku ya shawarci jama’a da su kai karar masu POS da ke tatsar su ta hanyar kiran CBN a lambobi kamar haka 07002255226; Ext: 711025 – 7; [email protected] da shafukansu na soshiyal midiya.
Karancin takardun naira na kara jefa yan Najeriya cikin wani hali inda mutane da dama ke kin amsar tsoffin kudi, yayin da wasu gwamnoni suka yanke shawarar maka gwamnatin tarayya a kotu don kalubalantar halin da ake ciki a jihohinsu.
Duk da mawuyacin halin da manufar sauya kudin ya jefa mutane a ciki, har yanzu akwai korafe-korafe kan rashin karfin sabis a tsarin biyan kudade ta yanar gizo wanda hakan ya sa ba a iya yin hada-hadar kudi ta hanyar transfa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here