Kin bin umarnin kotu kan batun canjin kudi zai iya kawo koma baya – Masana

0
216

Wasu masu ruwa da tsaki na gargadi kan rudanin da ka iya biyo bayan watsi da umarnin tsawaita lokacin cikar wa’adin daina amfani da tsoffin takardun Naira.

Biyo bayan kalaman Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, wanda ya ce wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na daina amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, 500 da 1000 na nan daram.

Sai dai masana shari’a da sauran masu ruwa da tsaki a kasar nan sun ce kin bin umarnin kotu da ya bai wa ‘yan kasa damar su ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har sai kotun ta yanke hukunci a kan lamarin, zai iya kawo yamutsi a kasar nan.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana wannan matsaya na babu gudu ba ja da baya a game da daina amafani da tsoffin takardun kudin ne a lokacin da yake zantawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Waje da ke birnin Tarayya Abuja a ranar Talata.

Emefiele ya ce an fara samun sauki a al’amarin karancin sabbin takardun kudi sosai tun lokacin da aka fara biyan kudaden a cikin bankuna wato baya ga samu a nau’urar ATM da kuma amfani da manyan wakilan CBN, yana mai cewa don haka babu bukatar yin la’akari da wani sauyi daga wa’adin ranar 10 ga Fabrairu.

Bayanin na Emefiele na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasa ke cikin rudani a game da umarnin kotun kolin da ta tsawaita wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu har zuwa ga lokacin da kotun za ta yi sauraren karar da gwamnonin uku daga Arewacin kasar nan suka shigar a gabanta.

Shin mene ne tanadin doka idan aka samu irin wannan sabani da ake gani inda bankin CBN ya ce ba zai sauya matsaya ba duk da umarnin kotun koli, Barrista Mainasa Kogo, a zantawarsa da VOA Hausa, ya ce kememe da gwamna Emefiele ya yi da kuma kin bin umarnin kotu zai iya kawo yamutsi a kasa kasancewa al’umma na cikin halin kakani-kayi.

Mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Mal. Baba Yusuf, ya bayyana cewa kememe da gwamna Emefiele ya yi ba laifinsa ba ne illa ‘yan Nijeriya su jira matsayin da shugaba Muhammadu Buhari zai dauka, inda ya yi kira da a duba halin ha’ula’i da ‘yan kasa ke ciki don saukaka musu wahalhalu da suka sha.

Ko yaya ‘yan kasa ke ganin wannan al’amari, Malam Ibrahim mai kantin sayar da kayayyakin amfani na yau da kullum ya ce suna cikin mawuyacin hali.

Wannan lamari dai ya haifar da zanga-zanga a wasu jihohin kasar nan, a wasu yankuna kuma gwamnatocin jihohi ne suka yo barazana ga duk wanda ya ki karbar tsofaffin takardun kudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here