Kotun koli ta dage sauraron kara kan canjin kudi

0
106

Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu Gwamnoni suka shigar kan canjin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa ranar Laraba mai zuwa.

Gwamnonin Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara ne dai suka garzaya kotun suna neman a hana bankin daina amfani da tsoffin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200 daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023.

Kotun dai, a yayin zamanta na ranar Laraba ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairin 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here