Yayin da ya rage kwana 10 cif a gudanar da babban zabe a Najeriya, har yanzu Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ba ta sami sabbin takardun kudaden da za ta yi amfani da su ba wajen biyan ma’aikatan wucin gadi ba.
Za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ’yan majalisun tarayya ne ranar 25 ga watan Fabrairu, sai kuma na Gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris.
’Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa da wahalar da suke sha sakamakon karancin sabbin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200, bayan sauya fasalinsu da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.
Sai dai a yau [Laraba] ne ake sa ran Kotun Kolin Najeriya za ta ci gaba da sauraron karar da wasu jihohi guda uku suka shigar da Gwamnatin Tarayya kan batun canjin kudin.
A makon da ya gabata dai, kotun ta hana gwamnatin aiwatar da daina amfani da kudaden daga ranar 10 ga watan Fabrairu, bayan Jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara sun shigar da kara.
A ranar Talatar da ta gabata kuma, Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi alkawarin samar wa hukumar sabbin kudaden don gudanar da zabukan yadda ya kamata.
Yadda karancin kudaden zai iya kawo cikas ga harkar zaben
To sai dai bayanai sun nuna har yanzu ba a ba hukumar sabbin kudaden ba, kamar yadda Kwamishinan INEC na yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Yahaya Bello ya yi korafi.
Ya ce yunkurin hukumar na gudanar da babban zaben zai iya fuskantar tasgaro daga karancin kudaden.
Da yake jawabi a Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki na shiyyar Arewa ta Tsakiya kan harkar zabe, wanda cibiyar CTA ta shirya, Yahaya ya ce hukumar na bukatar tsabar kudade don sallamar ma’aikatan wucin gadi da sauran ’yan kunji-kunji na ranar zabe.
Sai dai ya ce in ban da kalubalen rashin sabbin kudaden a kasa, hukumar tasu ta gama shiryawa tsaf don gudanar da zaben.
Ya ce ya zuwa yanzu, INEC tana da kusan kaso 80 cikin 100 na kayan aikin zaben, kuma tuni ta horar da ma’aikatan da za su yi aikin zaben mai zuwa.