Za a rataye masu gadi 2 kan aikata fashi da makami

0
48

Wata Babbar Kotun Jihar Ondo, ta yanke wa wasu mutane biyu Tasur Abubakar da Ayuba Idris hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsu da laifin aikata fashi da makami.

Kotun ta kuma samu mutanen biyu da laifin hada baki, inda ta yanke wa kowannensu hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

An gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu kan kisan Mista Kwaku Richard Kwakye da ‘yarsa mai shekaru 27, Tope Kwakye, a gidansu a ranar 1 ga Mayu, 2019, a rukunin gidaje da ke Ojomo Akintan, Olufoam a Akure.

Masu gadin sun amsa laifin kashe uban da ‘yarsa da kebir din babur kan tasirin shan miyagun kwayoyi, inda suka bayyana cewa sun shake su har lahira.

Lauyan jihar, John Dada, ya ce mutanen biyu Idris mai shekaru 24 da Abubakar mai shekaru 27, an gurfanar da su a gaban kotu bisa laifuka biyar.

A shekarar 2019, jami’an tsaro daga rundunar ‘yansandan jihar sun kama su kan kashe Kwaku Kwakye da diyarsa, Tope Kwakye.

Nan take aka gurfanar da su gaban kotu bisa laifuka biyar da suka hada da hadin baki, fashi da makami, da kuma kisan kai.

Ya ce laifukan da suka aikata ya ci karo da sashe na 6 (b), (1,2) (a) da (b), 324, 319, 319 (1) na dokar fashi da makami na dokokin Tarayyar Nijeriya na 2004.

Mai shari’a Williams Olamide, a hukuncin da ya yanke, ya yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutanen biyu da ake tuhuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here