Za mu gurfanar da wanda ya ƙi karɓar tsoffin kuɗi a gaban kotu – Gwamnan Legas

0
89

Gwaman jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya Babajide Sanwo-Olu ya gargaɗi duk waɗanda ke ƙin karbar tsofaffin takardun kuɗi a jihar da su daina yin hakan ko su fuskanci fushin shari’a.

Ya ce ƙin karɓar tsoffin takardun kuɗin ya saɓa wa matakin kotun ƙolin ƙasar .

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da tsare-tsaren kuɗi na jihar ya fitar ranar Laraba.

Gargaɗin na gwamnan na zuwa ne bayan kotun ƙolin ƙasar ta ɗage – sauraron ƙarar da wasu jihohin ƙasar suka shigar gabanta suna ƙalubalantar wa’adin Babban Bankin – zuwa 22 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ƙara da cewa ”a lokacin da zaman kotun na farko ranar 8 ga watan Fabrairu , kotun ta ce za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci game da lamarin”.

“Matakin yana nan bai sauya ba. Dan haka gwamnatin jiha ke gargaɗin mutanen da ke ƙin karɓar tofaffin kuɗin da su daina hakan, in ba haka ba kuma su fuskanci fushin shari’a”

”Saɓa doka ne ƙin karɓar tsofaffin kuɗin takardun kuɗi, kuma yin hakan ya saɓa wa matsayin umarnin kotu.’

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here