A karan farko sarki Sunusi ya ziyarci Kano

0
60

A karon farko tun bayan tube shi daga sarauta shekaru uku da suka gabata, tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci birnin Dabo a ranar Laraba.

Aminiya ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano ne a karon farko tun bayan tube rawaninsa.

Gwamnatin Jihar ce dai ta cire shi a ranar 9 ga watan Maris din 2020, saboda abin da ta kira da rashin girmamawa ga ofishin Gwamna Abdullahi Ganduje.

Bayanai sun ce ya yada zango ne a birnin Kano domin ya gaishe da mahaifiyarsa, yayin da yake hanyarsa ta zuwa Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, don yin ta’aziyyar rasuwar Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, sannan ya taya sabon Sarkin na Dutse murna.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here