Kotun musulunci ta aike da ‘yan TikTok gidan yari a Kano

0
146

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Filin Hockey a Kano ta tura matasa masu tashe a TikTok ciki har da Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Ragowar wadanda kotun ta tisa keyarsu zuwa gidan yarin sun hada da babban abokin Murja Kunya, wato Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi wakar ‘A Daidaita’.

Hakan kuwa na zuwa ne a yayin da ita Murja take cika mako biyu da zaman wakafi a gidan yari, a wata shari’a ta daban a gaban kotun.

A zaman kotun na ranar Alhamis ne Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ya ba da umarnin tisa keyar masu amfani da TikTok din zuwa gidan yari.

Tun da farko Majalisar Malaman Jihar Kano ta doka matasan ‘yan TikTok a gaban kotu kan zargin ba ta tarbiyya.

Da farko dai jami’an ‘yan sanda sun cafke Murja Ibrahim Kunya ana washegarin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta a jihar.

Sai dai Murka ta roki kotu da ta mata afuwa a gidan yari, yanzu haka alkalin kotun ya dage sauraren shari’ar zuwa mako mai aura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here