Hukumar kwastam ta kama haramtattun kaya da kudin su ya kai Naira miliyan 91.5 a Kebbi

0
101

Hukumar Kwastam ta Nijeriya, ta kama wasu kayayyaki da ake zargin an yi fasakwaurinsu ne da kudinsu ya kai Naira miliyan 91.5 a Kebbi.

Sabon shugaban hukumar a jihar, Mista Ben Oramalugo ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar na tsawon makonni biyu da suka gabata a Birnin Kebbi.

Kwastam

Ya ce nasarar da aka samu na kwace kayayyakin ta biyo bayan umarnin da ya bayar ga jami’an da ke sanya ido a kan manyan iyakokin da ke cikin jihar bayan ya karbi ragamar mulki a ranar 1 ga watan Fabarairu.

“Kokari da jami’an rudunar ke yi ya samar da sakamako mai kyau a ayyukan yaki da fasa-kwauri a jihar. A tsawon lokacin, mun sami nasarar kama wasu abubuwa daban daban har guda 14.

“Kayayyakin sun hada da Lita 8,975 na man fetur da aka loda a cikin jarka mai cin lita 25, buhunan shinkafar kasar waje 189, buhunan sukari 71 da aka shigo da su kasar waje, da dilolin gwanjo 42 da buhu 36 na takalman da aka yi amfani da su.

Kwastam

“Sauran sun hada da, kwali 74 na man sauya launin fata, batir mai amfani da hasken rana 110, katan-katan na magunguna 105, motoci bakwai da aka yi amfani da su wajen jigilar kayayyaki da kuma motar tanka daya da ake tsare da su. Kudin kayayyakin da aka ambata ya kai Naira miliyan 91.5,” in ji shi.

Har ilayau, mista Ben Oramalugo ya ce duk da irin makudan kudi da gwamnati ta biya domin samar da man fetur ga ’yan kasa a kan farashi mai sauki, wasu marasa kishin kasa sun zabi karkatar da kayan zuwa kasashen makwabta don amfanin kansu da kuma azurta kansu.

Ya kara da cewa, “Rundunar tana da duk wani kayan aiki da hukumar gudanarwar hukumar ta bayar a karkashin jagorancin Kanar Hamid Ibraheem-Ali, domin gudanar da aikinta kamar yadda dokar hukumar kwastam (CEMA) ta CAP C45 LFN, 2004 ta tanada.

Kwastam

“Musamman, sashe na 167 ya ba mu ikon kwace kayayyakin da aka shigo da su ba bisa ka’ida ba wanda ya saba wa dokokin da ba su dace ba,” in ji shi.

Bugu da kari mista Oramalugo ya ci gaba da bayyana cewa, hukumar ta gudanar da ayyukan hana fasa-kwauri don kare masana’antu na cikin gida da kuma karfafa tsaron iyakokin kasar domin ka da ‘yan ta’adda su shigo kasar.

Kwastam

“Ina so in yi amfani da wannan kafar wajen mika godiyarmu ga hukumomin ‘yan’uwanmu, da sauran sassan ma’aikata bisa goyon bayan da suke bayarwa da hadin gwiwar juna ta hanyar musayar bayanan sirri ga aikinmu na tabbatar da tsaron kasa.

Kwanturolan na Kwastam, ya yi godiya ga masu ruwa da tsaki da sauran jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here