Tsarin sauyin kudi ya taimaka wa ‘yan kasa wajen rage sharholiya da kudi – CIS Sunday

0
59

A cewarsa, yana da kyau al’ummar kasa su fahimci tsare-tsaren kasa da manufofinta tare da bukatun da suka shafi kasa; kasar nan tana tafiya ne bisa doron kundin tsarin mulki da ke jan ragamar kasar, kasar tana da kundin tsarin mulki da sauran dokokin da suke tafiyar da ita.

Kana ya ce akwai bukatar bangarorin doka su sake fayyace tsarin sauyin kudi domin kauce wa shafa wa gwamnati bakin fenti, babu wata gwamnatin da za ta dauki wani mataki ba tare da neman shawarorin rassan gwamnati da lamarin ya shafa ba.

Har ila yau, ya bayyana cewa, don maslahar kasa da hadin kanta, akwai bukatar a daina siyasantar da kowani lamari a kasar nan. An zo lokacin da ba a samun buhuhun kudade ko wadaka da kudade.

Ya kara da cewa, yana da kyau ‘yan Nijeriya su samu masaniyar dalilan sauya kudi. Hakan zai kawo karshen wafcen aljihu, kai hare-hare da balle motoci da gidaje a kowani lokaci domin neman kudi a hannun jama’a.

“A maimakon kushe tsarin, kamatuwa ma ya yi a jinjina ga matakin ba wai yin korafi ko zanga-zanga ba. Yana da kyau mu koyi yadda za mu ke amsar manufofin kasa domin ya fi karfin ra’ayoyin kashin kai.

“A matsayina na masanin harkokin tsaro, ina shawartar ‘yan Nijeriya da kada su mara baya wa duk wata manufar amfani da kudade ta gurbataccen hanya gabanin babban zaben kasa. Don me gwamnati ba za ta dakile yunkurin sayen kuri’a a lokacin zabe da watsa kudi ba da kuma bai wa jama’a kudi domin sayen ‘yancinsu.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasa kuma da bukatar a kara wayar wa al’umma da kai kan muhimmancin wannan sauyin kudin wanda masu kishin kasa za su gane kuma za su mara wa tsarin baya.” Ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here