Yadda karancin kudi ya shafi kananan sana’o’i

0
102

Shin wannan matsala da ‘yan Nijeriya suka shiga ta hada-hadar kudade tana shafar kananan sana’oi ko kawai masu mnayan kudade ne suke shan wahala? A ‘yan kwanakin nan babu abin da ludayinsa ke kan dawo irin tsarin sauya launin kudade a Nijeriya.

Kamar yadda kowa ya sani ne babban bankin Nijeriya wato CBN ya sauya launin takardun kudi wato takardar Naira 1000 da Naira 500 da 200. Kafin zuwa karshen watan Janairu duk ‘yan Nijeriya masu wadancan kudade sun garzaya bankuna don kai tsoffin kudade don musanyasu da sababbi.

Kowa na sane da yadda mutane suka shiga halin dimuwa da wahala wajen sauya takardun kudaden nasu. Sannan kuma yadda jama’ar Nijeriya suka dimauce ta neman kudade a hannu shima wani hali ne da ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu inda takardun kudi musamman sababbin suka zama kamar wasu gwalagwalai. A ranar Lahadin karshen watan Janairun wannan shekarar Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa ‘yan Nijeriya kwanaki goma don su ci gaba da sauran tsoffin kudaden da suke rage a hannunsu. Saboda kiraye kiraye da shugabanni suka yin a neman an janye shirin zuwa wani lokaci.

Majalisar dokokin kasa ta dattijai da ta wakilai suma sunyin nasun kokarin wajen jawo hankalin babban bankin Nijeriya don ya sauya tunani, wajen sauya launin kudin. A haka ne ita majalisar wakilai ta yi wani kudiri inda ta nemi tsarin sauya fasalin kudin ya kai watan Yulin wannan shekarar don bai wa ‘yan Nijeriya damar canja kudadensu don gudun asara.

Hakika wannan tsari na babban bankin Nijeriya ya zo wa da ‘yan Nijeriya wata sabuwar wahala wacce har yanzu take yi wa ‘yan Nijeriyar barazana na hana su yin kasuwanci cikin jin dadi da annashuwa. Kowa na tare da sanin cewa bankunan kasuwanci na Nijeriya sun taka muhimmiyar gudunmawa wajen kuma ta’azzara wannan wahala ga ‘yan Nijeriya.

Har ila yau wannan tsarin na babban bankin Nijeriya kamar yadda wasu masana tattalin arziki suka fada sun ce ba zai yi wa masu kananan sana’oi dadi ba musamman wadanda suka dogara kacokan wajen hulda da kudade a fili. Misali kowa ya sani cewa ‘yan kasuwa da suke sayar da abubuwan amfanin yau da kullum kamar kayan abinci da sauran kananan abubuwa wadanda sai dasu mutane suke samu suyi amfani da su don cin abinci. Kamar kayan miya da man girki da ake auna wa kadan-kadan akan karamin farashi da suaransu.

Irin wadannan sana’oi hakika da yawan ‘yan Nijeriya wadannan sana’o’in da su suka dogara. Saboda haka a wannan hali da ake cikin yanzu su irin wadannan kasuwanci su ne suke shan bugu saboda karancin kudade da yake hannun mutane. Sannan kuma kamar yadda na dada a baya su dai wadannan sana’oi yawanci masu yinsu ba su da asusun banki.

Ta haka ne ya sa da yawansu suke shan wahala wajen yin ta’ammali da mutane. Kamar yadda na ga wata mace a mota tazo tana sayen doya a wajen wani mai sayar da doyar bayan ta gama ciniki sai ta fadawa mai doya ya bata lamabar asusu za ta tura masa, a nan me doya ya ce ai shi sam bai san zance ba.

Haka matar nan tana ji tana gani ta hakura ta bashi doyarsa. Anan hakika wannan me doya ya yi rashin wannan ciniki saboda kawai ba shi da lambar akawunt na banki ko nace bashi da asusun banki.

Mutane da yawa ‘yan Nijeriya masu kananan sana’oi hakika suna da kalubale na mallakar asusun banki, saboda yadda su kansu bankunan ba sa samar da tsari me kyau wanda zai sa ‘yan Nijeriya su yi hulda da su. Kowa na sane da yadda yanzu shi kansa yadda aikin sabis na intanet ya ke wahalar da mutane wajen tura kudade zuwa asusun jama’a. Musanman lokacin da aka fara wannan aiki na sauya launin kudade.

Kananan sana’oi a kasashen da suka damu da ‘yan kasar suna yin tsari me kyau ta yadda duk wasu tsare tsare da aka kirkira a cikin kasa suna bawa ‘yan kasar dama ta yadda ba za su sha wahala ba ko kadan bayan samar da tsare tsare.

A nan ya zama dole ga gwamnatocinmu su rika saka ‘yan kasa a cikin tsare-tsarensu a duk lokacin da suka fito da wani sabon tsari don saukakawa ‘yan kasar. Kananan sana’o’i a duk kasashen duniya su ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki, duk sanda aka samu matsala wajen kula da wadannan sana’o’i to hakika jama’a da yawa za su ji jiki, kamar yadda yanzu ‘yan Nijeriya suke gani.

Sannan kuma ya zama dole muma ‘yan Nijeriya mu dawo daga tunani irin na da, domin rungumar ci gaba da duniyar fasaha take zuwa da su. Ya zama dole ga jama’a da su bude asusun ajiya a bankuna domin taimakon kasuwancinsu da kuma bai wa kudadensu tsaro mai inganci. Har’ila yau suma bankunan dole su samar da tsaro da karfin fasaha wajen kare dukiyoyin jama’a da don rungumar wannan tsarin na takaita amfani da kudade a fili.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here