Abun da ya sa manoma suka ki sayar wa da ‘yan kasuwa amfanin gonakan su

0
139

Rahotanni sun ce, wasu daga cikin manoma a wasu sassan kasar nan, sun mayar da amfanin gonakan su zuwa gida   saboda matsalar karancin tsabar kudade.

Sun kuma ki sayar da amfanin gona ga ’yan kasuwar da ke son tura musu kudin kayansu da suka saya ta bankin, saboda karancin takardun kudi.

A cewarsu, akwai masaya da suke zuwa don su tura kudaden ta asusun ajiyar banki, a amma mu ba za mu amince ba, domin idan aka tura mana ta banki, ba za mu sami takardun kudaden  ba,  inda suka kara da cewa, a yanzu suna a cikin halin kunci, don idan aka ce kasa babu kudin ai dole a shiga halin kunci, domin komai zai tsaya kamar yadda ta kasance a yanzu.

Sun bayyana cewa, lamarin a kasuwa babu dadi, domin duk wanda bai zo da kudi ba, sayen kayan amfanin gona zai yi masa wahala, inda suka sanar da cewa, masu sayen kaya, ba sa zuwa  da kudi domin suma a can ba su da kudin, domin duk inda kaje ko wurin masu POS ne babu kudi.

A cewar wasu manoman  farin wake da masara sun ce, suna ci gaba fuskantar  karancin takardun kudin, inda suka sanar da cewa, akwai masaya da suke zuwa don su tura kudaden ta asusun ajiyar banki, a amma mu ba za mu amince ba, domin idan aka tura mana ta banki, ba za mu sami takardun kudaden ba.

A cewarsu, muna cikin halin kunci, don idan aka ce kasa babu kudi  ai dole a shiga halin kunci, domin komai zai tsaya kamar yadda ta kasance a yanzu.

Wasun su kuwa, sun  ce ba su taba shiga irin wannan hali na tsaka mai wuya a kasuwar ba, inda suka kara da cewa, mutane utane kowa ya kawo kaya yana bukatar kudi, don biyan bukatarsa yana tsaye, amma ko kwabo ba mu samu ba. A cewar wasun su, sun isa  kasuwa da wuri sai dai, ba su iya sayar da komai ba domin babu kudi a hannun su.

Romanus Eze ya yi nuni da cewa, sababbin manoma na irin wannan kuskuren, amma wadanda suka jima  suna yi sun san irin wannan ruwan na wuri ba ma za a kira shi damina ba.

Shugaba Romanus ya bayyana cewa, don haka kada ganin yayyafi mai karfi ya sa manoma su fara shuka, don bata lokacinsu ne da kudadensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here