Iyalina abinci yana gagararsu, saboda karancin Naira – Orji Kalu

0
93

Bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Kalu ya ce shi da iyalansa sun fuskanci kalubale na karancin kudi, inda ya ce ba zai iya samun isassun kudin da zai iya yin girki a gidansa a kwanan nan ba.

Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin gidan talabijin na Channels, a kan zaben 2023 a ranar litinin.

“Kana ganin manufar ta yi daidai amma ba na ajiye kudi a gidana. Ina shan wahala.

“A kwanakin baya, manajan gidana ya gaya wa matata da ke Abuja cewa ba mu da kudin da za mu dafa abinci. Matata kusan tana yawo kuma muna ciyar da mutane sama da 250 kowace rana. Wannan matsala ce a gare ni da kuma ga kowa da kowa.”

Kalu ya koka kan karancin kudin da Naira ke fama da shi, sakamakon yadda babban bankin Najeriya CBN ya sake fasalin kudin kasar.

Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi kakkausan suka game da karancin takardun kudi bayan da babban bankin CBN ya yi na sake fasalin kudin kasar.

In zaku iya tunawa cewa Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa tsofaffin takardun kudi na N1,000, N500, da N200 na nan daram.

Amma, a makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita amfani da takardun kudi na N200 har zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023, wanda ya mayar da wasu a matsayin wadanda ba na doka ba.

Matakin dai ya harzuka gwamnoni da dama musamman na jam’iyyar APC mai mulki inda suka ce a yi amfani da tsofaffin takardun kudi a jihohinsu.

Kalu ya ce da ya yi biyayya ga umarnin kotun koli kan kudin Naira tunda Kotu ita ce gaba da  shugaban Najeriya.

Ya ce, “Don haka idan na kasance a matsayin shugaban kasa kamar yadda na fada muku a baya, zan saurari hukuncin kotun koli. Kotun koli a gare ni, ko suna da gaskiya ko ba daidai ba, ya kamata shugaban kasa ya bi doka kuma ya nemi babban lauyansa da ya sake duba Kotun Koli.”

Sanatan mai wakiltar Abia ta Arewa, ya ce tabarbarewar kudi ba za ta shafi damar jam’iyyarsa ta APC ba ta lashe zaben shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here