Mun shirya samar da tsaro a lokacin zabe – Janar Irabor

0
50

Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Lucky Irabor, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa rundunar soji da sauran jami’an tsaro a shirye suke su samar da tsaro a babban zaben 2023.

Irabor ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zanta wa da manema labarai jim kadan bayan gana wa da hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tsaro a ranar Litinin a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai (NAN), ya ruwaito cewa taron na sirri ya samu halartar hafsoshin tsaron kasar nan; Babban Sufeton ‘Yansanda, Daraktocin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), da kuma Babban Hafsan Tsaro (CDI).

Ya ce makasudin taron shi ne duba tsarin tsaro na zabe da kuma samar da tsare-tsare don tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana.

“Mun gana da hafsoshin tsaron, Sufeto Janar na ‘yansanda.

“Duba da batun tsaro na zabe kuma kamar yadda kuka sani, ‘yansanda ita ce kan gaba wajen tabbatar da tsaro a zabe, mun yi bayanin kula tare da tantance halin da ake ciki kuma mun shirya.”

Irabor ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su yi aiki a kowane bangare na kasar nan domin tabbatar da gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, ta yadda duk ‘yan Nijeriya da suka cancanta su yi amfani da damarsu.

Ya kara da cewa an dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro na musamman.

Ya gargadi wadanda ke da niyyar haifar da rikici a lokacin zaben da su kiyayi kansu domin za su fuskanci hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here