An ceto mutane 12 daga hatsarin mota, wasu sun kone kurmus a Ebonyi

0
59

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Ebonyi, ta ce ta ceto mutane 12 da wani hatsarin da ya rutsa da su a kan babbar hanyar Abakaliki zuwa Ogoja a ranar 18 ga watan Fabrairu.

Kwamandan hukumar a Ebonyi, Uche Chukwurah ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abakaliki a ranar Talata cewa jami’an hukumar sun kai wadanda aka ceto zuwa asibitin koyarwa na tarayya na Alex Ekwueme Abakaliki.

Kwamandan ta ce hatsarin ya afku ne a makarantar horas da malamai (TTC) da ke karshen titin yayin da wadanda abin ya shafa suka samu raunuka daban-daban.

“Mun kai dauki ranar 19 ga Fabrairu kuma an ba da rahoton cewa wadanda abin ya shafa suna karbar magani yayin da aka sallame wasu,” in ji ta.

Ta ce rundunar ba za ta iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a hatsarin ba sai dai iya wadanda suka jikkata.

“Hatsarin ya hada da motar bas da wata mota kirar Toyota Sienna kuma mun gano cewa motar ta kone.

“Mutanen motar bas din sun riga sun kone kurmus ta yadda ba za mu iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

“Ana zargin hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuke kima,” in ji Chukwurah.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa motar bas din ta nufi Taraba ne daga Ribas.

“Motar bas din ta kwace ne sakamakon kauce wa mai babur daga nan suka yi karo da motar Sienna.

“Motar bas din ta fashe sannan ta kama da wuta,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here