Canjin kudi: Kotun koli za ta ci gaba da sauraron karar da gwamnoni suka shigar

0
80

Kotun koli ta tabbatar da cewar dole ne a yau ta saurari karar takaddamar canjin kudi da wasu gwamnoni suka shigar da kara a kai.

Alkalan kotun su bakwai da mai shari’a alkali Inyang Okoro ya jagoranta ya sanar da cewa, kotun ba zai aminta da sabbin masu son shiga cikin karar ba, inda ya ce, dole ne su yi biyaya da hukuncin da kotun za ta yanke kan takardamar da aka shigar a gabanta na sabbin takardun kudaden.

A cewar Okoro, sabbin masu son shiga cikin karar, za su iya shigar da ta su sabuwar karar a kan takardamar bayan an kammala sauraren karar farko da aka shigar a gabanta.

Alkalan kotun sun mayar da martanin ne kan bukatar da Atoni-Janar na Jihar Abiya, ya gabatar wa kotun kan sshiga cikin karar, daidai da irin karar da gwamnatin Jihar Ribas ta shigar ta hannun lauyanta, Emmanuel Ukala (SAN).

Bayan karin jihohi 11 da ke son shiga karar tare da jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara, alkalan sun ci gaba sauraren ainahin karar da tun farko jihohi umu suka shigar a gabanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here